Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dalibai 364 na kasar Masar sun samu tallafin karatu daga gwamnatin kasar Sin a bana
2019-08-29 10:46:11        cri

Sashin kula da harkokin ilimi na ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Masar ya ce, a shekarar da muke ciki, gaba daya kimanin dalibai 364 na kasar Masar ne suka samu tallafin guraben karo karatu daga gwamnatin kasar Sin, hakan yasa Masar ta zama kasar dake sahun gaba a nahiyar Afirka da ta samu dalibai mafi yawa daga kasar wadanda suka samu tallafin guraben karatu daga kasar Sin.

Ofishin jakadancin Sin dake Masar ya shirya liyafar ban kwana da daliban Masar da suka samu kyautar guraben karo karatu daga gwamnatin kasar Sin na shekara ta 2019 zuwa 2020, inda jakadan Sin dake Masar Liao Liqiang da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar suka hallara.

Babban jami'in kula da harkokin ilimi na ofishin jakadancin Sin dake Masar Song Bo ya ce, hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin ilimi yana bunkasa cikin sauri a shekarun nan, daga zangon karatu na shekara ta 2019 zuwa ta 2020, gaba daya gwamnatin Sin ta samar da kyautar kudin karatu ga dalibai 364 a Masar, ciki har da dalibai masu digiri na uku 126, wadanda akasarinsu ke nazarin fannin kimiyya da fasaha.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China