Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin firaministan kasar Sin ya halarci taron dandalin raya makamashi mara gurbata muhalli na Taiyuan na bana
2019-10-23 10:02:29        cri

Mataimakin firaministan kasar Sin Han Zheng, ya halarci taron dandalin raya makamashi mara gurbata muhalli na Taiyuan na bana, tare da karanta sakon da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika don taya murnar bude taron.

Han Zheng ya nuna cewa, Sin na fatan hadin kai da sauran kasashe wajen nazarin kyautata tsarin makamashi da hadin kai ta fuskar makamashi karkashin shawarar "Ziri daya da hanya daya", ta yadda za su ba da gudunmawarsu wajen daidaita tsarin makamashin duniya baki daya, da kuma zurfafa hadin kai wajen kyautata makamashi, har ma da nacewa ga kasancewar bangarori daban-daban a duniya, sannan da sa kaimi ga bunkasuwar makamashi mai dorewa cikin hadin kai, da kuma kiyaye tsabtaccen makamashi, da tabbatar da yanayin muhalli mai kyau a duniya.

Mataimakin babban magatakardan MDD Liu Zhenmin ya ba da jawabi a bikin bude taron, inda ya jinjinawa gudunmawar da Sin take bayarwa wajen jagorantar duniya ta fuskar rage fitar da gurbataciyar iska, da tinkarar sauyin yanayi da kuma sa kaimi ga bunkasuwar makamashin da ake iya sabuntawa, yana mai cewa, majalisar na fatan kara tuntubar kasa da kasa kan bunkasuwar makamashi da more fasaha da dabara a wannan fanni, da kuma dukufa kan cimma muradun samun bunkasuwa mai dorewa na shekarar 2030.

Taken taron a wannan karo shi ne "Juyin juya hali ta fuskar makamashi da hadin kan kasa da kasa", wakilai fiye da 800 daga kasashe da kuma kungiyoyin kasa da kasa sama da 20 sun halarci taron. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China