Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gudanar da taron hadin kan kasa da kasa dangane da makamashi na shekarar 2019 a kasar Sin
2019-10-16 20:34:13        cri

Za a gudanar da taron hadin kan kasa da kasa dangane da makamashi kana taron makamashin wutar lantarki na Sin da Afrika na shekarar 2019 daga ran 4 zuwa 7 ga watan Nuwamba a kasar Sin. Wakilai fiye da 600, daga gwamnatocin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa da kamfanoni da jami'o'i sama da 60, za su halarci taron. Ministocin makamashin kasashen Afrika da jakadun kasashen Afrika dake kasar Sin fiye da 10 da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa fiye da 70 da manyan jami'an kamfanoni da masanan jami'o'i za su yi jawabai a taron. Ban da wannan kuma, za a gabatar da muhimman rahotanni guda biyu a taron, tare da kulla yarjejeniyoyin hadin kai, don karfafawa bangarori daban-daban gwiwar shiga aikin gina manyan ababen more rayuwa a duniya da ma nahiyar Afrika, da gaggauta bunkasa makamashi mai tsabta da hada kai wajen samar da tashoshin samar da wutar lantarki tsakanin kasashen daban-daban. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China