Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya taya murnar bude taron motoci masu amfani da makamashi mai tsabta na kasa da kasa na shekarar 2019
2019-07-02 11:39:27        cri

A yau ne, aka bude taron motoci masu amfani da makamashi mai tsabta na kasa da kasa na shekarar 2019 a birnin Boao na lardin Hainan, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika da sakon taya murnar bude taron.

A cikin wasikar, shugaba Xi ya nuna cewa, sana'ar kera motoci masu amfani da makamshi mai tsabta ta shiga wani sabon mataki dake saurin bunkasa, saboda ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasaha da kuma gyaran fuskar da ake yiwa sana'o'i daban-daban.

Ya ce, wannan mataki ba ma kawai zai samar da sabon karfin raya tattalin arzikin kasashe daban-daban ba, har ma zai taimaka wajen rage fitar da abubuwan dake gurbata iska, da tinkarar matsalar sauyin yanayi da kyautata muhallin hallitun duniya.

Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin na nacewa ga hanyar samun bunkasuwa mai dorewa ba tare da gurbata muhalli ba, kuma tana fatan kara hada kai da sauran kasashen duniya, don ingiza bunkasuwar aikin kirkire-kirkire na sana'ar motoci masu amfani da tsabtaccen makamashi da sauran sana'o'i masu ruwa da tsaki, ta yadda za su ba da gudunmawa wajen kiyaye muhallin duniya da kafa al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin Bil Adama. Shugaba Xi yana kuma fatan mahalarta taron za su kara tuntubar juna tare da cimma ga matsaya daya da zurfafa hadin kai a wannan sana'a, domin ganin nasarorin da aka samu ta fuskar ayyukan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha za su kawo alheri ga daukacin al'ummar duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China