Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Cibiyar raya makamashi ta Afrika za ta lalubo damarmakin kasuwanci a kasar Sin
2019-08-23 10:40:31        cri
Cibiyar raya makamashi ta Afrika (AEC) za ta ziyarci birnin Beijing na kasar Sin a mako mai zuwa, da nufin laluben damarmaki da bangarorin hadin gwiwa tsakanin Sin da nahiyar Afrika.

Cibiyar ta ce wakilanta, karkashin shugaban cibiyar Nj Ayuk, za su gana da shugabannin kamfanonin makamashi na gwamnati da masu zaman kansu da na kungiyoyin masana'antar.

Daraktan aiwatar da shirye-shirye na cibiyar, Mickael Vogal, ya ce suna samun karin adadin kamfanmonin kasar Sin dake son shiga cibiyar, musamman domin samun damarmakin zuba jari da sahihan bayanai kan kasuwar makamashi ta nahiyar.

Cibiyar ta ce yayin da jarin kasar Sin ke karuwa a Afrika, tana taimakawa kamfanonin kasar da dama wajen shiga kasuwannin makamashi na nahiyar da ke bunkasa cikin sauri.

Ta kara da cewa, yunkurin wani bangare ne na mara baya ga kara jan hankalin masu zuba jari dake neman yin kasuwanci a Afrika, galibinsu daga kasashen Sin da Rasha da India da Gabas ta Tsakiya da Turkiyya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China