Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu ruwa da tsaki a fannin makamashin Afrika sun tattauna makomar fannin
2019-10-10 09:55:26        cri
A jiya Laraba aka bude taron masu ruwa da tsaki a fannin albarkatun mai da lantarki na Afrika wato (AOP) karo na hudu a Cape Town na kasar Afrika ta kudu, da nufin tattauna matakan da za su kara ingiza ci gaban fannin makamashi don bunkasa ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Taron na kwanaki uku ya kunshi jami'an fannonin man fetur, iskar gas, da kuma lantarki, inda za su tattauna game da rawar da fannin makamashi zai taka wajen bunkasa sauran fannoni da gina hanyoyin ci gaban tattalin arzikin nahiyar.

Wasu bayanan da aka fitar a lokacin taron sun yi nuni da cewa, nahiyar Afrika tana daga cikin shiyyoyi mafiya girma a duniya da ake ci gaba da gano albarkatun mai da iskar gas. A shekarar 2016, biyar daga cikin goma na wuraren da aka gano albarkatun mai a shiyyar Afrika ne. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China