Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tsarin ilmin manyan makarantun Sin ya samu kyautatuwa cikin shekaru 20
2019-10-22 09:54:58        cri

Wani rahoton hukumar sanya ido kan dokokin manyan makarantun ilmi na kasar Sin ya bayyana cewa, tsarin ilmin manyan makarantun kasar ya samu gagarumin cigaba cikin shekaru 20 da suka gabata.

Tsarin ilmin manyan makarantun ilmin kasar Sin ya kara samun cigaba matuka a cikin shekaru 20 din da suka gabata, inda a cikin wannan wa'adin an samu yawan jami'o'i da manyan kwalejojin ilmi a fadin kasar Sin kimanin 2,663 ya zuwa shekarar 2018, inda ya ninka sama da sau 1.6 daga shekarar 1998, a cewar rahoton wanda aka gabatar a taron da ake gudanarwa a duk bayan watanni biyu-biyu na zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin (NPC).

Adadin dalibai Sinawa dake shiga manyan makarantun ilmin kasar Sin ya karu daga miliyan 8.5 a shekarar 1998, zuwa miliyan 38.33 a shekarar 2018, inda adadin ya karu da kashi 48% na daliban manyan makarantun 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 22 na haihuwa ya zuwa shekarar 2018, a cewar rahoton. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China