Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani babban jami'in JKS ya yi kira da a fadada cin gajiyar ilimi tsakanin Sin da sauran sassan duniya
2019-09-11 09:15:47        cri
Jami'in ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kuma shugaban sashen watsa labarai na kwamitin kolin jam'iyyar Huang Kunming, ya yi kira da a kara azama wajen yayata fahimtar juna, da gina alaka mai karfi, da za su haifar da karin damammaki na koyon fasahohin juna, da cin gajiya tare tsakanin Sin da sauran sassan duniya.

Huang Kunming, ya yi wannan kira ne a jiya Talata, a jawabinsa na bude taron kasa da kasa karon na 8, game da nazarin harkokin ilimi na kasar Sin.

Taron dai na da taken "Sin da sauran sassan duniya: ci gaba tare cikin sama da shekaru 70 da suka gabata". (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China