Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta tsara wani shirin bunkasa ilmi da masana'antu na gwaji
2019-10-11 09:53:45        cri
A jiya Alhamis kasar Sin ta wallafa wani shirin gwamnatin kasar na gwaji, wanda zai bunkasa fannonin ilmi da masana'antu da nufin inganta harkar cigaban ilmi, da zakulo mutane masu basira, da kyautata masana'antu, da kuma samar da ingantaccen ci gaban tattalin arzikin kasa.

A bisa shirin da aka tsara, kimanin biranen kasar 50 ne za su aiwatar da shirin na gwaji don bunkasa masana'antu da ilmi cikin shekaru biyar masu zuwa, kana za'a zakulo adadin masana'antun shiyya da suka yi fice wajen bunkasa ci gaban masana'antu da kuma fannin ilmi.

Gwamantin kasar Sin ta sha alwashin samar da kananan sana'o'i sama da 10,000 karkashin shirin na gwaji cikin wa'adin da aka kebe.

Karkashin wannan shirin, za'a bada fifiko wajen bunkasa ci gaba da samar da kudade, wadanda za'a kashe su wajen aiwatar da sauye-sauye ga tsarin samar da mutane masu basira da kuma rage tsadar kudaden tafiyar da ayyukan cibiyoyin kasar.

Shirin ya kuma jaddada aniyar aiwatar da cikakken tsarin bayar da kwarin gwiwa ta hanyar bada kyaututtuka kamar a fannonin kudi da na ilmi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China