Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana da malamu sama da miliyan 16
2019-09-04 09:27:17        cri

Ma'aikatar ilimi ta kasar Sin, ta bayyana cewa, kasar na da malamai kimanin miliyan 16.74, kuma kaso 79 cikin 100 na wannan adadi ya karu ne a shekarar 1985, lokacin da kasar ta ayyana ranar 10 ga watan Satumban ko wace shekara a matsayin ranar malamai ta kasa.

Ren Youqun, wani jami'i a ma'aikatar, ya bayyana yayin wani taron manema labarai jita Talata cewa, a cikin shekaru 35 da suka gabata, ingancin aikin malamanta a kasar ya karu matuka.

Jami'in ya ce, tun a shekarar 2012, an dauki sabbin dalibai da suka kammala karatunsu na jami'a guda 510,000 don su koyar a makarantun karkara dake yankunan tsakiya da kuma yammacin kasar Sin, wadanda ake koyar da tsarin ilimi na tilas, baya ga wasu maluma 250,000 da aka tura yankuna masu fama da matsanancin talauci.

Shi dai tsarin ilimi na tilas a kasar Sin, ya kunshi shekaru shida a makarantar firamare da kuma shekaru uku a karamar makarantar sakandare.

A cikin shekaru 35 da suka gabata, sana'ar malamanta ta kara samun daraja, inda albashin malaman ya inganta nesa ba kusa ba, har ya tashi daga matsayin da ake biyan maluman kafin shekarun 1980 zuwa matsayi na 7 cikin rukunin masu karbar albashi mafi kyau guda 19 a kasar Sin.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China