Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta gabatar da karin matakan kare 'yancin mallakar fasaha
2019-07-18 09:44:36        cri
Majalisar gudanarwar kasar Sin, ta amince da daukar karin matakan inganta kare 'yancin mallakar fasaha.

Sanarwar da aka fitar bayan kammala taron majalisar karkashin Firaministan kasar Li Keqiang, ta ce kasar za ta ci gaba da karfafa sanya dokar kare 'yancin mallakar fasaha da inganta jarrabawar samun 'yancin mallakar fasaha.

A cewar sanarwa, za a kare halaltattun hakkoki da muradun dukkan 'yan kasuwa bisa daidaito da adalci.

Har ila yau, kasar Sin, za ta gaggauta tsarawa da inganta matakan gano tamburan kayayyaki da kwaikwayon fasaha da kuma karfafa wayar da kai game da keta 'yancin mallakar fasaha da sanya hukunci mai tsauri ga kowane irin nau'i na keta ka'idoji.

Kasar za kuma ta karfafa hadin gwiwa da kasa da kasa kan kare 'yancin mallakar fasaha da mara baya ga kamfanoni wajen samu da kare yancin a kasashen waje. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China