Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin da Amurka sun shiga sabon zagayen tattaunawa a birnin Washington
2019-10-11 09:20:46        cri

A jiya Alhamis kasashen Sin da Amurka suka fara sabon zagayen tattaunawar tuntubar juna da nufin lalibo bakin warware takaddamar ciniki da tattalin arziki dake tsakaninsu.

Tawagar kasar Sin karkashin jagorancin mataimakin firaministan kasar Liu He, kuma mamban kwamitin harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, shi ne babban jagoran dake wakiltar bangaren kasar Sin a tattaunawar warware takaddamar ciniki da tattalin arzikin tsakanin Sin da Amurka, a bangaren Amurka kuwa, wakilin hukumar cinikin kasar Robert Lighthizer, da sakataren baitulmalin kasar Steven Mnuchin su ne ke wakiltar Washington.

Wannan muhimmin zagaye ne a tattauanwar neman warware takaddamar cinikin, za'a shafe ranakun Alhamis da Juma'a ana gudanar da tattaunawar. Tun a baya bangarorin biyu sun sha gudanar da makamanciyar tattaunawar sulhun na manyan jami'an kasashen biyu don samun maslaha. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China