Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta kakabawa wasu mutane da sassa masu alaka da Rasha takunkumi
2019-10-01 10:08:09        cri
Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, ya shelanta kakabawa wasu mutane da wasu sassa masu alaka da kasar Rasha takunkumi, bisa zargin su da yunkurin tsoma hannu cikin harkokin zaben rabin zango na Amurka wanda ya gudana a shekarar 2018.

Da yake bayyana wannan mataki cikin wata sanarwa a jiya Litinin, Mr. Pompeo ya ce takunkumin ya shafi wasu sassa 4, da daidaikun mutane 7 dake aiki a wata cibiyar bincike ta yanar gizo, tare da mai daukar nauyin cibiyar Yevgeniy Prigozhin.

Shi ma a nasa bangare, ofishin baitulmalin Amurka ya bayyana cewa, cibiyar binciken ta yanar gizo, ta rika amfani da sunayen bogi tana tura sakwannin karya ta kafafen sada zumanta na internet, da nufin haifar da tasiri ga zaben na rabin zangon na shakarar 2018.

Takunkumin dai zai shafi wasu kadarorin Mr. Prigozhin da shi kan sa, da ma wasu mutane ko sassa na Amurka da suka yi mu'amala da shi.

Alaka tsakanin Amurka da Rasha dai na kara tsami, tun bayan da sassan biyu suka samu sabani game da rikicin kasar Syria, da na Ukraine, da batun dakile yaduwar makamai, baya ga batun zargin da aka yiwa Rasha na tsoma hannu a zaben Amurka. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China