Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar wakilan Amurka ta bukaci hukumomin gwamnati su ba ta hadin kai game da binciken da take yi kan Donald Trump
2019-10-09 09:57:32        cri

Majalisar wakilan kasar Amurka ta bayar da sammaci daya bayan daya ga ma'aikatar tsaron kasar da hukumar kula da harkokin yau da kullum da kasafin kudi ta kasar a ranar 7 ga wata, inda ta bukaci su gabatar da wasu takardun dake da alaka da batun "buga waya" da shugaban kasar Donald Trump ya yi ga shugaban Ukraine, domin taimakawa majalisar a bincike da take na tsige Trump mukaminsa.

Wadannan sammaci biyu da aka bayar bayan kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar ya tuntubi kwamitocin kula da harkokin diflomasiyya da na sa ido da yin kwaskarima, ya ba ma'aikatar tsaron kasar, da hukumar kula da harkokin yau da kullum da kasafin kudi ta kasar, wa'adin kwanaki 15, su gabatar da takardun da za su taimaka wajen binciken dalilin da ya sa fadar White House ta haramta amfani da kudin tallafi kan kasar Ukraine da dai sauransu. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China