Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kiyaye zaman lafiya da tabbatar da adalci
2019-10-21 09:35:51        cri
Mataimakin shugaban hukumar kula da ayyukan soji na kwamitin tsakiya na JKS, Xu Qiliang, ya jaddada cewa, Rundunar sojin kasar Sin za ta ci gaba da zama runduna mai tabbatar da zaman lafiya da adalci ba tare da la'akari da duk karfin da za ta kara ba.

Xu Qiliang, wanda kuma mamba ne na hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, ya bayyana haka ne yayin liyafar maraba, ta taro karo na 9, na dandalin Xiangshan ta Beijing, da yammacin jiya.

Ya ce taron wanda aka kirkiro a 2006, ya kasance dandalin tattauna batutuwan tsaro na duniya, yana mai cewa, duniya na fuskantar sauye-sauyen da aka dade ba a gani ba, sannan zaman lafiya da kwanciyar hankali na bukatar tattaunawa mai zurfi da kuma hadin gwiwa.

Jami'in ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da daukaka tsarin huldar kasa da kasa karkashin dokokin MDD da mara baya ga dangantakar kasa da kasa da kuma inganta zaman lafiya da ci gaba da hadin gwiwa da kuma moriyar juna.

Ya ce kasar Sin na nacewa ga sabbin tunani wajen samar da cikakken hadin gwiwa da tsaro mai dorewa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China