Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gasar wasannin soji ta kasa da kasa ta Wuhan ya kafa tarihi
2019-10-18 16:04:34        cri
Da yammacin yau Juma'a ne za a bude gasar wasannin soji ta kasa da kasa a birnin Wuhan na tsakiyar kasar Sin. Gasar da za a yi karon farko a kasar Sin, ta riga ta kafa tarihi.

Za a nuna bikin bude gasar a dandali mafi girma na duniya ta hanyar amfani da majigi na zamani da wuta mai haske irin na LED domin tsara fasahar 3D.

Wannan ne karo na farko da za a yi gasar a wurin da ba sansanin soji ba. Inda aka kafa wani wurin tsugunar da 'yan wasa na musamman a Wuhan, wanda ke iya daukar mutane 10,000. Haka zalika a karon farko, za a gudanar da gasar a birni guda, kuma a karon farko, za a yi amfani da fasahar 5G da 4K da VR wajen watsa shirye-shiryen talibijin yayin gasar.

Gasar ta wannan karo za ta kunshi wasanni da 'yan wasa mafi yawa a tarihi, inda za a yi wasan badminton da kwallon tebur, har da wasan gymnastic na maza a karo na farko.

Jimilar sojoji 9,308 daga kasashe 109 ne za su fafata ta Wuhan, wadda ta kafa tarihi na yawan 'yan wasa cikin shekaru 24 na tarihin gasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China