Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kara ba da ilimin sanaoin hannu ga sojojin da suka yi ritaya
2019-09-06 10:24:35        cri

Hukumomin kasar Sin za su kara ba da damar samun ilimin sana'o'in hannu ga sojojin da suka yi ritaya, a wani kokari na inganta samar musu aikin yi da fara sana'o'i da tabbatar da samar da cikakken aikin yi ga mazan jiyan.

Wata sanarwar hadin gwiwa da ma'aikatun ilimi da na kula da harkokin mazan jiya da na harkokin kudi suka fitar, ta ce ana karfafawa tsoffin sojin gwiwar neman gurbin karatu a kwalejojin koyar da sana'o'i.

Sanarwar ta ce za a samar da sharrudan samun gurbin karatu da jarrabawar neman gurbi na daban ga kwalejojin, domin tsoffin sojojin.

Ta kara da cewa, ba kamar sauran masu neman gurbin karatu ba, za a daukewa tsoffin sojojin jarrabawa, amma kuma za a yi musu gwajin basira da intabiyu.

Haka zalika, tsoffin sojojin na iya shiga makarantun sakandare dake koyar da sana'o'in hannu ba tare da sun yi jarrabawar neman gurbin karatu ba. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China