Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun yi garkuwa da jami'in dan sanda a Najeriya
2019-10-21 09:21:28        cri
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da yin garkuwa da wani babban jami'inta a ranar Asabar a jahar Kaduna dake arewacin kasar.

Musa Rambo, mataimakin kwamishinan 'yan sanda mai kula da tsakiyar arewacin birnin Suleja, ana zargin masu garkuwa sun yi awon gaba da shi a babbar hanyar jahar Kaduna, kakakin hukumar 'yan sandan jahar Yabuku Sabo, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua faruwar lamarin.

Sabo bai yi karin haske game da batun garkuwar ba, sai dai ya ce an samu bayanai daga bangaren masu garkuwar dake neman a biya su kudin fansa wanda kakakin bai ce uffan kan lamarin ba.

Wata majiyar jami'an tsaro ta fadawa Xinhua cewa, masu garkuwar sun bukaci a biya su Naira miliyan 50 kwatankwacin dala 140,000 a matsayin kudin fansa kafin su sako jami'in dan sandan. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China