Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An hallaka masu tada kayar baya 39 a Zamfara cikin mako guda
2019-10-13 16:06:15        cri
Kakakin sojojin Najeriya ya ce a kalla 'yan bindiga 39 aka hallaka kana wasu dama aka raunata cikin mako guda yayin wasu ayyukan sintiri a karo biyu wadanda dakarun sojojin Najeriya suka kaddamar a jihar Zamfara dake shiyyar arewa maso yammacin kasar.

An kaddamar da ayyukan sintirin ne a yankunan Bakura da Anka dake jihar, Oni Orisan, kakakin rundunar sojoji ta musamman ta Operation Hadarin Daji shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Ya ce an kashe 'yan bindigar 19 a lokacin arangamar da aka yi tsakaninsu da sojoji a dajin Anka yayin da aka hallaka 'yan bindigar 20 a yankin Bakura.

Orisan ya nanata cewa, sojojin ba za su kai hari kan duk wasu 'yan bindigar da suka tuba suka aje makamansu ba, amma wadanda suka yi kunnen kashi suke dauke da bindigogi kuma suke yin gangami su ne ake dauka a matsayin 'yan tada kayar baya.

Ya jaddada kira ga mayakan da ba su tuba ba da su gaggauta mika wuya kuma su mika makamansu ga hukumomin da abin ya shafa kana su rungumi shirin wanzar da zaman lafiya wanda gwamnatin jahar ta bullo da shi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China