Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliyar ruwa ta afkawa tsakiyar Najeriya ta hallaka mutane 10
2019-10-17 09:13:25        cri
Wani jami'in yankin ya sanar da cewa, mamakon ruwan sama a shiyyar tsakiyar Najeriya ta haifar da mummunar ambaliyar ruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe mutane a kalla 10.

Da yake bada tabbacin faruwar lamarin ga manema labarai a jiya Laraba, Ibrahim Inga, shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Nija a tsakiyar Najeriya ya ce, an samu hasarar rayukan ne sama da watanni biyun da suka wuce.

Ya ce an samu ambaliyar ruwan ne a yankunan sakamakon ruwan sama da aka samu ba tare da kakkautawa ba mai hade da iska tun daga watan Augasta, lamarin da ya haddasa tumbatsar koguna da koramu a yankin.

A cewarsa, kimanin gidaje 2,714 ne ambaliyar ruwan ta lalata. Mutane 21, 223 ne ambaliyar ruwan ta shafa a kananan hukumomi 20 na yankin, yayin da al'ummomi 123 ne suka fuskanci ambaliyar ruwan.

Hukumar hasashen ruwan sama ta Najeriya, ita ce ke da alhakin yiwa jama'a gargadi game da batun ambaliyar ruwan, a wannan shekarar, an yi hasashen jahohin Najeriyar 36 da babban birnin kasar Abuja ne za su fuskanci ambaliyar ruwan. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China