![]() |
|
2019-10-14 10:15:10 cri |
Femi Oke-Osanyintolu, janar manajan hukumar bada agajin gaggawa ta jahar Legas ya shedawa kafafen yada labarai cewa, al'amarin ya faru ne a ranar Asabar din da ta gabata a sakamakon mamakon ruwan sama da aka sheka a yankin.
Ya ce wata mace da 'yayanta uku sun mutu a sanadiyyar ruftawar ginin sai dai mijin matar ya tsira da ransa.
Oke-Osanyintolu ya ce, ginin dake kan tudu ne ya rufto kan wani gida dake kasa, sai dai a cewarsa ba'a tabbatar da adadin mutanen da birabizan ginin ya danne ba, amma masu aikin ceto suna cigaba da gudanar da ayyukansu.
Wani kwararre a yankin ya ce, ana yawan samun matsalolin ruftawar gini a Najeriya sakamakon yadda wasu masu tsara gine gine basa mutunta dokokin da suka shafi aikin tsara gine ginen.
A mafi yawan lokuta, ana jibga abubuwa masu nauyin gaske a saman ginin, kuma a wasu lokutan ana amfani da kayayyakin gini marasa inganci. (Ahmad)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China