Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu hasarar rayuka a ruftawar gini a Najeriya
2019-10-13 16:24:49        cri
Gwamnatin jahar Legas dake Najeriya ta ce an samu adadin da ba'a tantance ba na mutanen da suka mutu a sanadiyyar ruftawar gini a yankin Magodo dake jahar.

A wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, wasu jami'an sa'ido wadanda gwamnatin jahar Legas ta tura sun tabbatar da cewa ginin ya rufta ne sanadiyyar mamakon ruwan sama.

Sanarwar ta ce, ba'a tantance adadin mutanen da suka mutu ba. Sai dai tuni jami'an kai dauki gaggawa sun riga sun ziyarci wajen domin kai dauki.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatarwa Xinhua cewa ginin ya rufta kana ya fado kan wani gida, inda ya hallaka wata mace da 'ya'yanta 3 a lokacin da suke barci.

Ana yawan samun matsalolin ruftawar gini a Najeriya kasancewar wasu daga cikin jami'an dake aikin gine-gine ba su mutunta dokokin da suka shafi aikin tsara gine-gine ba, a cewar wasu kwararru a yankin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China