Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yara 'yan kasa da shekaru 5 ne suka dauki kaso 49 na masu fama da tamowa a Nijeriya
2019-10-18 09:31:29        cri
Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya ce kaso 49 na yara 'yan kasa da shekaru 5 a Nijeriya, kasa mafi yawan al'umma a Afrika, na fama da tamowa kuma ba sa girma yadda ya kamata.

Cikin wata sanarwa da ta shiga hannun Xinhua a Abuja, UNICEF ta ce irin wadannan yara na fama da kiba fiye da kima ko kuma rashin girma, tana mai cewa, rashin abinci mai gina jiki shi ne babbar matsalar da kiwon lafiyar al'umma da ci gaba ke fama da ita a Nijeriya.

UNICEF ta kara da cewa, ya kamata a magance matsalar, tana mai kira da gwamnatin tarayya da bangarori masu zaman kansu da masu bada gudunmuwa da iyaye da dangi da ma 'yan kasuwa, su taimakawa yaran su girma yadda ya kamata.

A cewar hukumar, wasu matakai da za su taimaka wajen inganta yanayin sun hada da kara zuba kudi ga shirye-shiryen dake da nufin kare tamowa a tsakanin yara da tallafawa wajen kulawa da su idan matakan kariyar sun gaza aiki da kuma tallafawa mata masu shayarwa wajen ciyarwa da kulawa da 'ya'yansu yadda ya kamata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China