Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 3 sun mutu wasu 7 sun bace yayin da kwale-kwale ya kife a tekun Kamaru
2019-08-27 10:00:37        cri
Kimanin mutane 3 ne suka mutu kana wasu mutanen 7 suka bace bayan da wani kwale-kwale ya kife a tekun Bakassi Peninsula dake kudu maso yammacin jamhuriyar Kamaru da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda jami'an tsaron tekun Kamaru suka bayyana.

Laftanal Kanal Emmanuel Sone, jami'i mai kula da tekun Kamaru ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua da yammacin ranar Litinin cewa, sun yi nasarar ceto mutane 107, sai dai abin takaici sun gano gawarwakin mutane 3 a wajen.

A cewar Laftanal Kanal Sone, mutane 117 ne a cikin kwale-kwalen, kuma mutane 7 din da suka bace wata kila sun makale ne a jikin jirgin ruwa. Wata majiya da ta bukaci a sakaye sunanta daga kamfanin jirgin ruwan Achouka ta tabbatarwa Xinhua adadin fasinjojin dake cikin jirgin ruwan.

To sai dai kuma, gidan talabijin na kasar Kamaru CRTV, ya sanar a yammacin Litinin cewa, fasinjoji 40 ne suka bace. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China