Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamaru ta bayyana yankuna masu magana da Turanci da arewa mai nisa a matsayin shiyyoyi masu barazanar tattalin arziki
2019-09-03 12:56:46        cri
Firaministan jamhuriyar Kamaru Joseph Dion Ngute, ya sanya hannu kan wata dokar dake ayyana yankunan kasar da suka hada da arewa maso yamma, kudu maso yamma, da yankin arewa mai nisa a matsayin shiyyoyi masu barazanar tattalin arziki.

A bisa dokar wacce bata bayyana takamammun karin matakan da za'a dauka ba, tace duk wasu kamfanonin dake gudanar da ayyukansu a shiyyoyi dake da barazanar tattalin arzikin za'a dage musu biyan haraji har na tsawon shekaru uku.

A watan Yuli, ministan raya tattalin arziki da bunkasa cigaban yankunan kasar Alamine Ousmane Mey, ya bayyana cewa shirin muradun samar da dawwamamman cigaban kasar yana fuskantar tarnaki sakamakon matsalar tsaro da ta dabaibayi yankuna biyu masu magana da yaren Turanci dake shiyyar arewa maso yamma da kudu maso yammacin kasar inda mayakan 'yan aware ke fafutukar neman kafa kasarsu, sai kuma matsalar rikicin Boko Haram dake addabar yankin arewa mai nisa.

Alkaluman da gwamnatin kasar ta fitar sun nuna cewa, matsalar tashe tashen hankula dake addabar yankunan masu magana da yaren turanci yayi sanadiyyar rufe kamfanoni kimanin 20, ko dai rufewa ta wucin gadi ko kuma ta dindindin.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China