Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mayakan BH sun kashe sojoji 5 a Kamaru
2019-09-16 11:17:02        cri
Sojojin Kamaru a kalla 5 aka kashe, yayin wani bata kashi tsakaninsu da mayakan BH, a ranar asabar da dare, a yankin Soueram na arewa mai nisa na kasar.

Rundunar sojin kasar, ta ce mayakan sun kona gidaje da dukiya, tare da farwa sansanin soji dake yankin.

Wani hafsan soji da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Xinhua cewa, wasu sojoji 9, da suka hada da sojin ruwa 5 da 'yan sandan soji 4, sun jikkata yayin harin. Kana an kwashe makamai tare da lalata sansanin.

Ko a ranar Juma'a, mayakan sun kashe fararen hula 2 a Kerawa na yankin arewa mai nisa.

An kashe sama da mutane 2,000, tun bayan da BH ta kaddamar da kai hari a yankin arewa mai nisa na Kamaru a shekarar 2014. Duk da hare haren da ake kai wa yankin lokaci zuwa lokaci, an samu raguwarsa cikin shekara 1 da ta gabata. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China