Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun damke kwamandojin Boko Haram 10
2019-10-13 15:27:00        cri
A jiya Asabar rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da kama kwamandojin kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram su 10 wadanda take nemansu ruwa a jallo a jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, yayin da suka yi yunkurin tserewa sai dakarun sojojin suka yi musu dirar mikiya.

An samu nasarar farautar mayakan ne a ranar Laraba a kauyen Bitta dake yankin karamar hukumar Gwoza karkashin jami'an sojojin runduna ta musamman ta 26 wanda hakan ya yi sanadiyyar aka kai ga kama wadanda ake zargin, a cewar Aminu Iliyasu, jami'in dake rikon mukamin kakakin rundunar sojojin.

Ya ce mafi yawan wadanda aka kama din sun bayyana kansu da cewa suna tuka motocin yaki da mayakan Boko Haram suka yi amfani da su wajen shirya mummunan harin nan da aka kaddamar a Gwoza a shekarar 2014.

Iliyasu ya ce dakarun sojojin Najeriyar sun tsaya tsayin daka wajen gudanar da aikin kakkabe ayyukan ba ta gari a lungu da sako na kasar. Ya ce jami'an sun samu nasarori masu yawan gaske a ayyuka daban daban da suka gudanar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China