Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar kara kokari wajen yakar talauci
2019-10-17 19:50:51        cri
Xi Jinping, babban sakataren kwamitin koli na JKS, ya jaddada bukatar kara zage damtse wajen ganin an yi nasara a yakin da ake yi da talauci.

Xi wanda har ila, shi ne shugaban kwamitin kolin na sojojin kasar, ya bayyana haka ne, cikin wani umarni da ya bayar a yau Alhamis, yayin da kasar ta Sin ke bikin ranar yaki da talauci karo na 6, ranar da ake bikin ta a ranar 17 ga watan Oktoban kowa ce shekara.

Ya ce, wajibi ne kasar Sin ta yi kokarin cimma burinta na kawar da talauci, da kara kokari, da tabbatar da samun sakamako mai inganci a yaki da talauci.

Shugaba Xi ya kuma yaba da irin ci gaban da aka samu, wajen kawar da talauci karkashin jagorancin JKS, yana mai cewa, yakin da kasar take yi a wannan fanni, ya shiga wani muhimmin mataki na ganin an kammala shi tare da samun nasara.

Xi ya kara da cewa, wajibi ne dukkan yankuna da sassa, su mayar da hankali wajen cimma manufofin da aka sanya a gaba, da ci gaba da kara zage damtse wajen ganin bayan kangin talauci, da inganta yankunan dake sahun baya a fannin tsarin ba da ilimi tilas, muhimman kayayyakin kiwon lafiya, gidaje da ruwan sha mai tsafta ga al'ummomi masu fama da talauci, da tabbatar da cewa, dukkan masu fama da talauci dake yankunan karkara, sun fita daga talauci, ta yadda nan da shekara mai zuwa, za su shiga rukunin al'umma mai matsakaicin makoma. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China