Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi da Macron za su yi hadin gwiwa kan batun gamayyar kasa da kasa da warware kalubalolin duniya
2019-10-16 12:50:02        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron sun zanta ta wayar tarho a jiya Talata, kana sun amince za su yi hadin gwiwa da juna game da batun gamayyar kasa da kasa da kuma warware kalubalolin dake tunkarar duniya.

Xi ya fadawa Macron cewa, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da manufarta ta bude kofa domin cin moriyar juna, kana za ta ci gaba da yin aiki tare da al'ummomin kasashen duniya, ciki har da jama'ar kasar Faransa, da nufin gina wata al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama.

A nasa bangaren, Macron ya taya shugaba Xi murnar cika shekaru 70 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, yana mai cewa, kasashen Faransa da Sin sun jima suna cin gajiyar dangantakar dake tsakaninsu.

Macron ya ce, a shirye yake ya ci gaba da yin musayar ra'ayi da shugaba Xi da kuma duba yiwuwar sake kai ziyara kasar Sin a nan gaba.

Shugabannin kasashen biyu sun kuma yi musayar ra'ayoyi game da batutuwan da suka shafi kasa da kasa da na shiyya shiyya.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China