Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Na'urar harba tauraron dan adam ta kasar Sin samfurin Smart Dragon-1 ta tafi duniyar obit a karon farko
2019-08-17 16:20:06        cri
Da misalin karfe 12:11 na rana agogon Beijing a yau Asabar, sabuwar na'urar dake daukar tauraron dan adam samfurin Smart Dragon-1 (SD-1), wanda aka kera ta don harkokin kasuwanci, ta yi tashin farko inda ta dauki taurarin dan adam 3 zuwa duniyar orbit.

Rokar, da kamfanin China Rocket Co. Ltd ya kera, karkashin kulawar kwalejin fasahar kera tauraron dan adam ta kasar Sin (CALVT), ya harba na'urar ne daga cibiyar harba tauraron dan adam ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin

Tauraron dan adam din guda 3, dukkansu kamfonin dake birnin Beijing ne suka kera su, kuma za'a yi amfani da su ne wajen ayyukan gano yankuna, da harkokin sadarwa, da kuma fannin ayyukan intanet.

Sabanin na'urar harba roka samfurin Long March, sabon samfurin na Dragon an kera su ne don biyan bukatun 'yan kasuwa da nufin harba kananan taurarin dan adam na kasuwanci, kamar yadda shugaban kwalejin CALVT Wang Xiaojun, ya bayyana.

Na'urar SD-1, tana da tsawon mita 19.5, da fadin mita 1.2, kuma tana da karfin da za ta iya daukar nauyin da ya kai ton 23.1, tana da kananan fika-fikai wanda za ta iya harba nauyin da ya kai kilogram 200 zuwa duniyar obit a nisan gudun kilomita 500. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China