Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yadda Amurka ke neman ta da zaune-tsaye a Hong Kong zai illata moriyar kanta da ta wasu
2019-10-16 15:54:52        cri

Jiya Talata ne majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da shirin doka dangane da hakkin dan Adam da Demokradiyya a shekarar 2019 a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin. Kasar Sin ta bayyana tsananin fushi da adawa da matakin.

Yanzu ana kara fahimtar cewa, ya zama tilas a kwantar da kura a Hongkong, da maido da oda da tabbatar da aiwatar da doka a yankin nan da nan ba tare da wani jinkiri ba. A wannan lokaci, wasu mutanen Amurka na tsoma baki cikin harkokin Hong Kong, a yunkurin dakatar da ci gaban kasar Sin, maimakon neman samarwa Hong Kong da alheri.

A shekarun baya, Amurka ta fi sayar da kayayyakinta zuwa Hong Kong, gwargwadon kayayyakin da Hong Kong ke sayar mata. A shekarar 2018 kawai rarar kudin cinikin da ke tsakanin Amurka da Hong Kong ta kai dalar Amurka biliyan 33.8.

Ban da haka kuma, idan ba a samu wadata da kwanciyar hankali a yankin na Hong Kong ba, tabbas za a illata moriyar kamfanonin Amurka fiye da 1300 da ke tafiyar da harkokinsu a Hong Kong, kana kuma za a kawo illa ga Amurkawa dubu 85 da ke aiki da zama a Hong Kong. Saboda haka, yadda majalisar wakilan kasar Amurka ta zartas da shirin doka dangane da hakkin dan Adam da Demokradiyya a shekarar 2019 a yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin zai illata moriyar kasar Amurka ita kanta gami da moriya ta wasu bangarori. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China