Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Na'urorin sarrafa sinadarin Uranium na zamani guda 40 sun fara aiki a Iran
2019-09-08 16:37:53        cri
Kakakin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Behruz Kamalvandi ya shirya taron manema labaru a yau Lahadi a Tehran, inda ya yi bayani sosai kan mataki na uku da kasarsa ta dauka daga ranar 6 ga wata, game da rage abubuwan dake cikin alkawarin da ta cika bisa yarjejeniyar makamashin nukiliyar kasar. Behruz Kamalvandi ya bayyana cewa, kasar ta riga ta fara gudanar da ayyukan na'u'rorin sarrafa sinadarin Uranium guda 40 na zamani, don amfanawa wasu ayyukan nazarin kimiyya da fasaha. Ya kuma jaddada cewa, wadannan na'urorin, sun fi wadanda kasar ta taba amfani da su a baya inganci.

Bayan da kasar Iran ta sanar da hakikanin abubuwan dake cikin matakinta na uku, kasashen Rasha, Burtaniya, Faransa da kuma Amurka sun mayar da martani daya bayan daya a ranar 7 ga wata. Wakilin kasar Rasha dake hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya(IAEA) ya bayyana cewa, bai kamata a sanya wasu ra'ayoyi na daban cikin wannan matakin da Iran ta dauka ba, domin ba zai kawo hadarin yaduwar makamashi ba. A nata bangaren, kasar Burtaniya ta nuna bacin rai sosai kan batun. Ita kuwa kasar Faransa cewa ta yi, za ta ci gaba da kalubalantar Iran don ta bi yarjejeniyar nukiliyar kasar a dukkan fannoni. Amurka kuwa ta ce, matakin da Iran ta dauka ba abun mamaki ba ne, saboda a ko da yaushe, take yarjejeniyar makamashin nukiliyar take yi. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China