Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
IRGC: Makamai masu linzami na Iran za su iya kaiwa ga sansanonin soja Amurka dake yankin
2019-09-16 10:08:18        cri
Kwamandan sashen kula da harkokin sararin samaniya na dakarun juyin-juya hali na kasar Iran (IRGC) Amir Ali Hajizadeh, ya bayyana cewa, makamai masu linzami na kasarsa, za su iya isa sansanonin sojan Amurka dake yankin.

Ya ce, baya ga sansanonin sojan na Amurka, makaman na Iran, za su iya kaiwa ga jiragensu na ruwa, ciki har da masu daukar jiragen sama da ma jiragen yaki dake nisan kilomita 2,000, suna kuma sanya ido a kansu.

Jami'in na Iran ya bayyana cewa, mayakan saman kasarsa, sun kakkabo wani jirgin Amurka maras matuki dake leken asiri a yankin kudancin ruwan kasar a watan Yunin. Kuma Iran ta yi hakan ne, domin kare sararin samanta.

Don haka, ya ce, kullum Iran a shirye take ta fafata babban yaki da Amurka. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China