Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Iran ya kalubalanci Amurka da ta dakatar da matsawa kasarsa lamba
2019-09-19 13:47:56        cri
Kamfanin dillancin labaru na IRNA na kasar Iran ya ruwaito shugaban kasar Hassan Rouhani yana kalubalantar kasar Amurka da ta yi watsi da matakanta na matsawa kasarsa lamba.

Rahotanni na cewa, Rouhani ya bayyana a yayin taron majalisar ministocin kasar da aka shirya a Tehran, cewa idan Amurka tana son yin shawarwari tare da Iran, to kamata ya yi ta dakatar da duk wasu matakai na matsin lamba, yana mai cewa, duk wani yunkurin cimma buri ta hanyar matsa lamba, ba zai yi nasara ba.

Ban da wannan kuma, kamfanin dillancin labarai na IRNA ya bayar da labari cewa, ma'aikatar harkokin wajen kasar, ta isar da sako ga Amurka ta ofishin jakadancin kasar Switzerland dake Iran, inda ta yi gargadi cewa, za a mayar da martani kan duk matakan yaki da Iran da za a dauka bisa dalilin wai an kai hari kan matatun man Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta sake nanata cewa, Iran ba ta da hannu a wannan lamari. Don haka, ta yi allah wadai da ma adawa kan zargin da shugaban kasar Amurka Donald Trump da sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo suka yi mata. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China