Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Duniya ba za ta kama hanyar fatattakar talauci ya zuwa 2030 ba
2019-07-10 10:59:29        cri

Wani rahoton MDD ya ce, la'akari da yadda raguwar talauci ke tafiyar hawainiya, duniya ba za ta dauki hanyar kawo karshensa ya zuwa shekarar 2030 kamar yadda ajandar maradun ci gaba masu dorewa ke buri ba.

Rahoton muradun ci gaba masu dorewa na shekarar 2019, ya ce yawan matsanancin talauci a duniya ya ragu daga kaso 35.9 cikin dari a shekarar 1990, zuwa kaso 9.9 cikin dari a shekarar 2015. MDD ta bayyana matsanancin talauci a matsayin rayuwa kan kudin da bai kai dala 1.90 ba a kowacce rana.

Duk da gagarumar raguwar da aka samu, hasashen da aka yi ya nuna cewa, kaso 6 cikin dari na al'ummar duniya za su ci gaba da kasancewa cikin matsanancin talauci ya zuwa shekarar 2030, idan aka ci gaba da tafiya a yadda ake yanzu.

Rahoton ya kara da cewa, daga cikin mutane miliyan 736 da suke cikin matsannacin talauci a shekarar 2015, miliyan 413 sun kasance a yankin dake kudu da hamadar Sahara na nahiyar Afrika. Kuma wannan adadi na ci gaba da karuwa a shekarun baya bayan nan, sannan ya dara jimilar adadin matalauta na sauran sassan duniya baki daya.

Hasashe ya yi nuni da cewa, idan ba a samar da ingantattun manufofi ba, matsanancin talauci zai ci gaba da zama a yadda yake a nahiyar Afrika ya zuwa shekarar 2030. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China