Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Zazzabin shawara ya hallaka mutane 16 a arewacin Najeriya
2019-09-30 11:08:01        cri
Wata majiya daga jihar Bauchi a arewacin Najeriya, ta ce yawan mutanen da zazzabin shawara ya hallaka a jihar ya kai mutum 16. Majiyar ta ce yawan wadanda suka rasu ya karu daga mutum 7 a farkon watan nan, sakamakon watsi da allurar rigakafi da wasu mutane suka yi.

A cewar shugaban hukumar kula da lafiya a matakin farko na jihar Bauchi Rilwanu Mohammed, a ranar Alhamis ne aka samu mutum na baya bayan nan da ya rasu, sakamakon kamuwa da cutar. Ya ce "Mun lura cewa dukkanin mutanen da suka rasu sun ki amincewa a yi masu allurar rigakafin wannan cuta, maimakon hakan, a kan kai su ga masu magungunan gargajiya, yayin da marasa lafiyar ke cikin wani mawuyacin hali."

Jami'in wanda ya zanta da kamfanin dillancin labarai ta Xinhua, ya ce mafi yawan wadanda suka kamu da zazzabin na shawarar 'yan asalin karamar hukumar Alkaleri ne.

A ranar 3 ga watan Satumbar nan ne dai, cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya, ta ayyana bullar cutar a hukumance, a wannan yanki na arewacin Najeriya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China