Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya tana neman masu zuba jari a muhimman ayyukan fannin albarkatun man kasar
2019-10-10 09:41:31        cri

Babban kamfanin kula da albarkatun mai na Najeriya NNPC ya sanar a jiya Talata cewa, a shirye yake ya yi hadin gwiwa da dukkan cibiyoyin kudade da za su dauki nauyin gudanar da muhimman ayyuka a wannan fanni.

An bayyana hakan ne a lokacin ganawar jami'an gudanarwar babban kamfanin mai na Najeriya wato (NNPC), da ma'aikatan bankin shigi da fici na Afrika (Afreximbank) a Abuja.

Mele Kyari, manajan daraktan rukunin kamfanin na NNPC, wanda ya karbi bakuncin tawagar, ya bayyana cewa muhimman ayyukan da za'a gudanar sun hada da gyaran matatun man fetur na kasar da gina muhimman kayayyakin rijiyoyin man kasar da suka hada da aikin shimfida bututun mai. Kyari ya bayyana cewa, kamfanin ya bude kofarsa ga cibiyoyin kudi da kwararru domin yin hadin gwiwa tare da muhimman cibiyoyin kudade kamar bankin na Afreximbank domin bunkasa kamfanin man kasar.

Mataimakin shugaban bankin Afreximbank, Anthony Kamel, ya ce, jami'an bankin sun bayyana farin cikinsu bisa damar da kamfanin mai na NNPC ya ba su, a matsayinsa na muhimmin bangaren da ya shafi tattalin arzikin Najeriya wanda shi ne mafi girma a Afrika.

Ya kara da cewa, ziyarar za ta kara zurfafa matakan hadin gwiwa a tsakanin bangarorin wajen bunkasa fannin albarkatun mai da iskar gas a kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China