Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane 3 da Boko Haram ta yi garkuwa da su
2019-10-08 10:27:55        cri
Rundunar sojojin Najeriya tace tayi nasarar ceto mutane uku wadanda mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram suka yi garkuwa da su a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mutanen sun yi nasarar kubuta daga hannun mayakan na Boko Haram ne, bayan musayar wuta da aka yi tsakanin sojojin da 'yan ta'addan a kauyen Firgi dake garin Bama ta jahar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, kakakin rundunar sojojin Col. Aminu Iliyasu, shine ya tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa, sojojin sun kwato wasu motoci makare da kayan abinci a lokacin musayar wutar, mayakan sun yanke shawarar tserewa tare da barin motocin nasu bayan da sojojin suka karya lagonsu a lokacin fafatawar.

A wani cigaban kuma, sojojin sun tabbatar da damke wasu shahararrun masu garkuwa da mutane su 4 a jihar Rivers mai arzikin mai a lokacin da sojojin suka kaddamar da simame kan maboyarsu.

Mutanen suna cikin jerin sunayen wadanda hukumomin tsaron Najeriya ke nema ruwa a jallo, inji kakakin sojojin, ya kara da cewa, ana cigaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargin. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China