Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar zazzabin shawara a Nijeriya ya kai 26
2019-09-27 13:59:07        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar barkewar zazzabin shawara a jihar Ebonyi na yankin kudu maso gabashin Nijeriya, ya karu zuwa 26.

A cewar rahoton da WHO ta fitar jiya dangane da barkewar cutar na baya-bayan nan, cikin watanni 2 da suka gabata, cutar ta bazu zuwa yankunan kananan hukumomin jihar 9.

Ya zuwa ranar 30 ga watan Augusta, an samu mutane 84 da ake zargin sun kamu da ita, inda adadin wadanda suka mutu sanadiyyarta ya kai kaso 31.

Hukumar ta ce, duk da Nijeriya ta sanya allurar rigakafin zazzabin shawara cikin jerin alluran rigakafin yara a kasar a shekarar 2004, galibin wadanda suka mallaki hankalinsu na da rauni, kuma garkuwar baki dayan al'ummar kasar ya yi kasa.

Tsakanin watan Janairu da Yuli, mutane sama da 2,000 ne aka yi zargin sun kamu da zazzabin a yankunan kananan hukumomi 506 daga jihohi 36 na kasar, ciki har da babban birnin tarayya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China