Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mataimakin shugaban Najeriya ya sha alwashin wanke kansa a kotu
2019-09-26 20:48:03        cri
Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Yemi Osinbajo, ya sha alwashin daukar matakan shari'a, domin tabbatar da ya wanke kansa daga zargin aikata cin hanci da rashawa, bayan da wata kafar watsa labarai ta yayata wani zargi da aka yi masa.

Mr. Osinbajo ya bayyana hakan ne a jiya Laraba, yana mai cewa ya shirya jingine rigar kariyar shari'a da yake da ita, domin gurfana a gaban kuliya, tare da wadanda a baya bayan nan, suka yayata zargin sa da aikata cin hanci ko almundahana.

Wata kafar watsa labarai ta kasar ce dai ta rawaito tsohon babban mataimakin kakakin jam'iyyar APC mai mulkin kasar, na cewa Mr. Osinbajo ya karbi wasu makudan kudade daga hukumar tattara harajin kasar, da nufin amfani da su wajen gudanar da yakin neman zabe, yayin babban zaben kasar da ya gabata. To sai dai kuma tuni hukumar tattara harajin ta karyata wannan zargi.

Mr. Osinbajo ya bayyana wannan zargi da cewa, ba shi da tushe balle makama, kuma karya ce tsagwaron ta, aka kaga domin bata masa suna. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China