![]() |
|
2019-10-09 16:22:38 cri |
Yau Laraba a nan Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Solomon Islands Manasseh Sogavare, inda ya nuna cewa, kasashen biyu sun kulla huldar jakadanci a tsakaninsu a hukumance bisa tushen mutunta ka'idar "kasar Sin daya tak a duniya", abin da ya yi tafiya daidai da lokaci da kuma kawo wa jama'ar kasashen biyu alheri.
A nasa bangaren kuma, Manasseh Sogavare ya ce, kasarsa ta amince da ka'idar "kasar Sin daya tak a duniya", ta yi abin da yawancin kasashen duniya suka yi, kuma abin da ta yi ya yi daidai a tarihi. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China