Xi Jinping zai halarci kwarya-kwaryar tattaunawa karo na 2 tsakanin shugabannin Sin da India
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar a yau Laraba cewa, bisa gayyatar da firaministan kasar India Narendra Modi da shugaban kasar Nepal Vidya Devi Bhandari suka yi masa, a tsakanin ranakun 11 zuwa 13 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai tafi India don halartar kwarya-kwaryar tattaunawa karo na biyu tsakanin shugabannin Sin da India, kana zai kai ziyarar aiki kasar Nepal. (Bilkisu)
Labarai masu Nasaba