Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu nazarin al'amurran sun ce sassauta yakin ciniki tsakanin Sin da Amurka zai amfanawa Afrika
2019-07-07 16:57:28        cri
Yunkurin baya bayan nan na neman warware takaddamar ciniki tsakanin Sin da Amurka wanda ake fatan ya kasance a nan gaba, lamarin zai yi matukar haifar da alheri ga kasuwancin kasa da kasa kana zai amfanawa kasashen Afrika, wasu masu sharhin al'amurra ne suka bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Amurka Donald Trump, sun amince a ranar 29 ga watan Yuni cewa, zasu sake dawo da tattaunawa da kuma tuntubar juna game da batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu bisa matakin daidai wa daida da mutunta juna. Wannan wani muhimmin cigaba ne na cimma daidaito tun bayan da Washington ta dauki mataki na kariyar ciniki kuma ta dinga sauya matsayarta, lamarin da ya haifar da yakin ciniki tsakanin manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Cavince Adhere, wani mai nazarin alakar Sin da Afrika dake Nairobi, ya ce matakin abin a yi maraba da shi ne saboda zai kawo sassauci ga tattalin arzikin duniya.

Eric Mang'unyi, wani mai nazari ne a jami'ar Walter Sisulu dake Afrika ta kudu, yace sanarwar da aka fitar wasu alamu ne dake nuna an fara samun cigaba tun bayan da dangantaka tayi tsami tsakanin bangarorin biyu a 'yan watannin da suka gabata.

Masu nazarin sun lura cewa, kasar Amurka ce ta fara tayar da yakin cinikin, lamarin dake haifar da mummunar illa ga kasuwanci da tattalin arzikin duniya.

A watannin da suka gabata, cibiyoyin kasa da kasa, kamar asusun bada lamuni na kasa da kasa IMF, da bankin duniya, sun rage hasashen karuwar tattalin arzikin nahiyar Afrika bisa la'akari da barkewar yakin cinikin Sin da Amurka, kuma babu wani bangare da zai amfana muddin takaddamar tattalin arzikin kasashen biyu ta ci gaba.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China