Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyoyin 'yan kasuwan Amurka sun bukaci a daidaita takaddamar cinikayya dake tsakanin kasarsu da Sin
2019-08-24 16:23:33        cri
Kungiyoyin 'yan kasuwan Amurka, sun bukaci a daidaita takaddamar cinikkaya da Amurka ta tayar tsakaninta da Sin, yayin da Beijing ta sanar da sanya karin haraji kan kayayyakin Amurkar, inda ita ma Washington, ta ci alwashin mayar da martani.

Cikin wata sanarwa da cibiyar bunkasa cinikayya ta Amurka ta fitar, wadda ta nemi kasashen biyu su koma teburin sulhu, cibiyar ta ce dangantakar bangarorin biyu cikin shekaru 40 da suka gabata ta kasance ta moriyar juna mai ma'ana da kuma amfani.

A cewar Myron Brilliant, mataimakin shugaban cibiyar kuma shugaban sashen kula da harkokin waje na cibiyar, sun yi ammana ci gaba da dangantaka mai ma'ana tsakanin kasashen 2, ita ce hanyar da ta dace, domin ba sa son ganin kara tabarbarewar dangantakar Sin da Amurka.

Wata sanarwa da kungiyar kamfanonin Amurka dake cinikayya da kasar Sin USCBC ta fitar, ta ce ta fusata da sakon da shugaba Donald Trump ya wallafa a shafinsa na Tweeter a jiya, inda ya ci alwashin mayar da martani kan kasar Sin.

Kungiyar ta USCBC ta ce, al'ummar Amurka da yawansu ya kai miliyan 2.3 zuwa miliyan 2.6 ne ke aiki karkashin tsarin cinikayya da jarin Sin da Amurka, tana mai cewa ma'aikatan Amurka da manoma da masu sayayya da kamfanonin ne karuwar takkadamar za ta yi wa illa.

A jiya Juma'a ne, Shugaba Trump ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa, gwamnatinsa za ta yi kari kan harajin kaso 25 da ta sanya akan kayayyakin Sin dake shiga kasar da darajarsu ta kai dala biliyan 250 zuwa kaso 30, sannan karin harajin kaso 10 kan sauran kayayyakin da darajarsu ta kai dala miliyan 300, wanda zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Satumba, zai karu zuwa kaso 15.

Kungiyar manoman Amurka dake rajin tabbatar da ciniki cikin 'yanci, ta ce tankiyar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ta haifar da janyewar kasuwa a kasar Sin, lamarin da ya sanya manoman Amurka ke gab da asarar rarar cinikin amfanin gona da sauran sassan duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China