Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara taimakawa yankunan cinikayya cikin yanci na gwaji
2019-07-04 10:08:03        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana cewa, kasarsa za ta bullo da matakan da za su taimakawa yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji (FTZ), a wani mataki na zurfafa gyare-gyare da kara bude kofa ga kasashen waje da ma saukaka cinikayyar yanar gizo tsakanin kasashe.

An dauki wannan mataki ne, yayin taron majalisar zartarwar kasar na ranar Laraba da firaministan ya jagoranta. Wata sanarwa da aka fitar bayan kammala taron, ta bayyana cewa, kasar Sin za ta karfafawa yankunan cinikayya cikin 'yanci na gwaji gwiwa na kasancewa a kan gaba wajen kawar da shingayen dake hana ruwa gudu a bangaren harkokin mulki, da inganta ayyukan hidima da bunkasa harkoki na kirkire-kirkire.

Sanarwar da cewa, za kuma a bullo da karin matakai da nufin bunkasa harkokin cinikayyar yanar gizo tsakanin kasashe, matakin da zai kara bunkasa masana'antun kasar, da bunkasa kasuwa da bangaren hidima da samar da ayyukan yi.

Bugu da kari, taron ya yanke shawarar kara ba da kariya ga 'yancin mallakar fasaha a bangaren cinikayyar yanar gizo tsakanin kasashe da yaki da kayayyaki na jebu da masu karya dokoki.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China