Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta bukaci Amurka da ta daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe yayin babbar muhawarar MDD
2019-09-25 20:28:40        cri

A yau Laraba ne kakakin ma'aiktar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a nan Beijing cewa, babban taron MDD, ba dandali ba ne na soke-soke, da tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen duniya. Ya kuma jaddada cewa, kasashen Sin da Amurka, za su ci gajiyar juna muddin sun hada kansu, yayin da ba za su samu komai ba, muddin suka nuna wa juna kiyayya. Ya ce ba yadda za su yi, sai dai su girmama juna, da neman samun daidaito, duk da kasancewar bambancin da ke tsakaninsu.

Geng Shuang ya fadi hakan ne dangane da labarin da aka bayar cewa, a ranar 24 ga wata, shugaban Amurka Donald Trump ya sha ambato kasar Sin, cikin babbar muhawarar babban taron MDD, inda ya zargi kasar Sin da gazawa wajen cika alkawarin da ta yi, yayin neman shiga kungiyar ciniki ta duniya, kana ya yi fatan Sin za ta daidaita batun Hong Kong yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China