Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan jarida sama da dubu 4 za su watsa rahotanni game da gasar wasannin motsa jiki ta soja ta birnin Wuhan
2019-10-10 14:43:11        cri
Rahotani daga taron manema labarai da aka shirya game da gasar wasannin motsa jiki ta sojojin kasa da kasa karo na 7 na cewa, ya zuwa yanzu, kimanin 'yan jarida guda 4130 ne suka yi rajista don watsa rahotanni game da gasar ta wannan karo, adadin da ya kasance mafi yawa a tarihin gasar.

Za a gudanar da gasar wasannin soja karo na 7 daga ranar 18 zuwa 27 ga watan nan a birnin Wuhan na kasar Sin, kuma yanzu an shirya tsaf don gudanar da gasar.

Haka kuma, bayanai na nuna cewa, akwai 'yan jarida 258 daga kasashen Rasha, Jamus, Amurka da Koriya ta Kudu da suka yi rajista don watsa labarai game da gasar

A yayin gasar, za a kafa dandalin musaya a cibiyar watsa labarai ta yadda 'yan jaridun Sin da ketare za su iya yin shawarwari, an kuma shirya matakan hira da mahalarta gasar, an kuma gayyaci 'yan jaridu da su ziyarci wuraren shakatawa dake birnin Wuhan, ta yadda za su kara fahimtar al'adun wannan birni. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China