Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CGF ta zabi sabbin shugabanni
2019-09-06 10:35:00        cri

A jiya ne, babban taron hukumar shirya gasar wasannin kasashe renon Ingila na shekarar 2019 da ya gudana a birnin Kigalin kasar Rwanda, ya zabi sabbin mambobin hukumar gudanarwa da na kwamitin wasannin hukumar.

An sake zabar Louise Martin daga yankin Scotland, inda za ta ci gaba da rike mukamin shugabar hukumar a wa'adi na biyu na shekaru 4. An fara zabarta a wannan mukamin ne a shekarar 2015, inda ta zama mace ta farko da ta rike wannan mukami a tarihin hukumar shirya wasannin kasashe renin Ingila.

A jawabin da ta gabatar bayan sake zabarta a wannan mukami, Martin ta ce, tana alfahari da tarin nasarorin da jami'an hukumar da 'yan wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Commonwealth suka cimma, a jerin gasannin da hukumar ta shirya, da yadda suka tunkari kalubale da ma damammakin da suka yi amfani da su.

Kimanin wakilai 300 daga kasashe da yankuna 71 daga kasashen renon Ingila na Commonwealth ne suka halarci babban taron, da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Satumba.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China