Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
FIBA ta sanar da sunayen kasashe 24 da za su halarci gasar Olympic ta Japan
2019-09-20 11:05:06        cri

A jiya ne, hukumar kula da harkokin wasan kwallon Kwando ta duniya (FIBA) ta sanar da sunayen kasashen da ma jerin jadawalin matsayin kasashen a fagen wasan kwallon Kwando na duniya, bayan kammala gasar wasan kwallon Kwando ta duniya da kasar Sin ta dauki bakunci.

Kasashen Spaniya da Faransa da Argentina, da Amurka da Australiya da Najeriya da kuma kasar Iran sun cancanci halartar gasar wasannin Olympics da za a yi birnin Tokyo na kasar Japan. Kasar Japan za ta shiga gasar kai tsaye.

Za a tababtar da ragowar kasashe 4 da za su shiga gasar wasannin Olympics ta Tokyo ta hanyar shiga gasar ta neman shiga gasar wasannin Olympics mai zuwa, inda kasashe 16 mafiya kwarewa da hukumar ta zabo daga gasar cin kofin kwallon Kwando na duniya da kasashe biyu dake sahun gaba a wannan wasa daga Turai da Afirka da Americas, da Asiya da Oceania bi da bi za su yi takara da juna.

Kasar Sin mai masaukin gasar ta bana, ta kare a matsayi na 24 a gasar, kana ta 27 a jerin jadawalin hukumar FIBA, matakin da ya ba ta damar halartar gasar ta neman shiga gasar wasannin Olympics, a matsayin daya daga cikin kasashe biyu dake kan gaba a fagen wasan kwallon Kwando a yankin Asiya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China