Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An tabbatar da kungiyoyi 8 mafiya gwaninta a AFCON
2019-07-09 14:03:28        cri

A ranar 8 ga wata, a cikin wasanni 2 na karshe da aka yi domin fid da kungiyoyi 8 mafiya gwaninta a cikin gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin Afirka wato AFCON, kungiyar kasar Tunisiya ta yi kunnen doki da kungiyar kasar Ghana da ci 1 da 1 cikin mintoci 120, amma ta lashe kungiyar Ghana ne ta hanyar bugun daga kai sai mai tsaron gida da ci 6 da 5 a karshen wasan. Sa'an nan kuma, kungiyar Kodivwa ta lashe kungiyar kasar Mali da ci 1 da 0.

Za a ci gaba da wasannin fid da kungiyoyi 4 mafiya gwaninta a ranar 10 da 11 ga wata, inda kasar Senegal za ta yi takara da kasar Benin, kasar Nijeriya za ta yi takara da kasar Afirka ta Kudu, Kodivwa za ta yi takara da kasar Algeriya, kana kasar Madagascar za ta yi takara da kasar Tunisiya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China